Tarayyar Turai (EU) ta yaba wa Jihar Kano kan kokarin da take yi wajen bunkasa samar da abincin warkar da yara masu fama da matsananciyar tamowa, tana mai cewa hadin gwiwar gwamnati, masu zuba jari da kungiyoyin raya kasa na taimakawa wajen ceton rayuka da inganta tattalin arziki.
Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Mignot, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wata masana’antar NutriK’s da ke Kano, wadda ke samar da Ready-to-Use Therapeutic Food (RUTF), wani nau’in abinci na musamman da ake amfani da shi wajen kula da yara masu fama da matsananciyar tamowa.
Mignot ya ce samar da irin wannan abinci a Kano ya nuna yadda saka hannun jari da hadin gwiwar ci gaba za su iya taimakawa wajen magance matsalolin jin kai cikin gaggawa.
“Kayayyakin da ake samarwa a nan suna taimakawa yara masu bukatar kulawa, tare da nuna yadda kirkire-kirkire da yanayin kasuwanci mai kyau da gwamnatin Kano ta samar ke taimakawa wajen ci gaban al’umma da tattalin arziki,” in ji shi.
Ya kara da cewa manufar ziyarar ita ce kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Tarayyar Turai, UNICEF, gwamnatin Kano da kamfanoni masu zaman kansu domin inganta shirye-shiryen yaki da matsalar tamowa a Najeriya.
Kamfanin NutriK’s, wanda reshen kamfanin Nutriset na kasar Faransa ne, ya bayyana cewa yana kokarin kara amfani da albarkatun da ake samarwa a cikin gida wajen kera kayayyakinsa.
A halin yanzu kamfanin na amfani da gyada da ake shigowa da ita daga kasashen waje saboda matsalolin inganci a wasu kayayyakin cikin gida, amma ya ce yana zuba jari domin inganta sarrafa kayan noma a Najeriya.
Manajan Daraktan NutriK’s, Abdoulkader Yonli, ya ce amfani da kayan cikin gida zai rage kudin samarwa tare da bunkasa sarkar darajar noma daga manoma zuwa masana’antu.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu bukatar RUTF a Najeriya ta fi karfin yawan abin da ake samarwa, musamman ganin yadda yara da dama ke fama da matsananciyar tamowa.
Kididdigar UNICEF ta nuna cewa kusan yara miliyan biyu a Najeriya na fama da matsananciyar tamowa, matsalar da ke bukatar kulawa cikin gaggawa ta hanyar abinci na musamman irin na RUTF.
Masu ruwa da tsaki sun ce kara karfin masana’antun cikin gida, inganta ka’idojin noma da bunkasa yankunan masana’antu kamar Kano Free Trade Zone na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma tabbatar da wadatar abinci mai gina jiki na doon lokaci.
