Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta kama wasu mutane biyu tare da kwato motoci biyu da aka sace a wasu samame daban-daban da ta gudanar a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, CSP Eno Ikoedem, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce an kwato mota ta farko ne a ranar 22 ga Yuni, 2026, yayin wani binciken ababen hawa (stop-and-search) da jami’an ‘yan sanda suka gudanar a kan titin Siluko da ke Benin City.
Sanarwar ta ce jami’an da ke aiki a sashen Textile Mill Road Division sun tare wata ƙaramar mota kirar Daihatsu Hijet mai launin toka, mai lambar rajista GBZ 646 YK, inda binciken farko ya nuna cewa takardun motar da direban ya gabatar na bogi ne.
Bayan ƙarin bincike, an gano cewa motar mallakin Dr. Timothy Etinosa ce, wanda ya bai wa wani mai suna Emmanuel Afolayan motar bisa tsarin haya da mallaka (hire-purchase). Sai dai Afolayan ya gudu da motar tun a shekarar 2024, ya ƙirƙiri takardun bogi sannan ya sayar da ita.
Rundunar ta ce an kama direban motar, Ezikiel Aguele, mai shekaru 46, wanda bayan tambayoyi ya jagoranci jami’an zuwa kamo babban wanda ake zargi, Emmanuel Afolayan. Haka kuma an sake gano wata mota ta biyu da aka sace.
‘Yan sandan sun bayyana cewa mutanen biyu sun amsa laifin da ake zarginsu da shi, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
A nasa bangaren, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Edo, CP Monday Agbonika, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin saboda ƙwarewa da jajircewarsu.
Ya ce ci gaba da gudanar da binciken ababen hawa na daga cikin muhimman dabarun hana aikata laifuka, gano masu laifi, da kuma kwato kadarorin da aka sace.
Haka kuma ya bukaci al’umma su ci gaba da bai wa ‘yan sanda haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen yaƙi da aikata laifuka a fadin jihar.
