Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyarar girmamawa ga tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Saifullahi Hassan, ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa Obasanjo, wanda ke Kano domin wata ziyarar aiki, ya karbi bakuncin Kwankwaso a inda yake sauka a jihar.
Ta ce, “Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar NDC, ya kai ziyarar girmamawa ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a mazauninsa na wucin gadi da ke Kano.”
Rahotanni sun nuna cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, shi ma ya halarci ganawar.
Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba, ziyarar na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa da manyan ‘yan siyasa ke ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaben shekarar 2027.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu karin bayani daga bangarorin biyu kan sakamakon ganawar.
