Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun kalubalanci rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) wanda ya nuna raguwar jarin kasashen waje da ya shigo fannin sadarwa, suna masu cewa rahoton bai bayyana cikakken girman kudaden da ake zubawa a bangaren ba.
NBS ta bayyana cewa jarin kasashen waje da ya shigo fannin sadarwa ya ragu da kashi 91 cikin 100, daga dala miliyan 80.78 a shekarar 2025 zuwa dala miliyan 7.24 a zangon farko na shekarar 2026.
Sai dai kungiyar Kamfanonin Sadarwa Masu Lasisi ta Najeriya (ALTON) ta ce alkaluman sun mayar da hankali ne kawai kan jarin kasashen waje, ba tare da la’akari da kudaden cikin gida da ribar da kamfanoni ke sake zubawa wajen fadada ayyukansu ba.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ALTON, Gbenga Adebayo, da Sakataren Yada Labarai, Damian Udeh, suka sanya wa hannu, kungiyar ta bayyana cewa fannin sadarwa ya kashe kudin da ya kai Naira tiriliyan 2.13 wajen fadada ayyuka da inganta kayayyakin sadarwa a shekarar 2025.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa an shirya kashe karin Naira tiriliyan 1.86 a shekarar 2026 domin fadada cibiyoyin sadarwa da inganta ayyukan intanet da wayar salula a fadin kasar.
ALTON ta ce wannan ci gaba ya samu ne sakamakon matakan tallafin gwamnati, musamman amincewa da karin kudin kiran waya da na bayanai (data) da kashi 50 cikin 100 da aka yi a shekarar 2025.
A cewar kungiyar, karin kudin ya taimaka wajen farfado da kamfanonin sadarwa daga matsin tattalin arziki da suka fuskanta sakamakon hauhawar farashin aiki da faduwar darajar naira.
Kamfanonin sun kuma yi kira ga Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Babban Bankin Najeriya (CBN) da NBS da su samar da sabon tsarin tattara bayanai da zai rika nuna dukkan nau’ikan jarin da ake zubawa a fannin sadarwa.
ALTON ta ce hakan zai kara inganta fahimtar masu zuba jari kan hakikanin halin da bangaren sadarwa ke ciki tare da nuna gudunmawar da yake bayarwa ga tattalin arzikin dijital na Najeriya.
