Farashin danyen mai ya ƙara tashi a kasuwannin duniya yayin da rikicin da ke tsakanin Iran da ƙawayenta ke ƙara kamari, lamarin da ya haddasa fargaba kan samar da mai da zirga-zirgar jiragen ruwa.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta mayar da martani ga duk wani hari da aka kai kan cibiyoyinta, yana mai cewa, “Ido da ido” ne manufar tsaron ƙasar.
A gefe guda kuma, bayanan harkokin jiragen ruwa sun nuna cewa akalla jiragen ruwa tara sun dakatar da tafiyarsu ta mashigar Bab al-Mandab bayan ‘yan tawayen Houthi sun sanar da kakaba takunkumi kan tashoshin jiragen ruwa na Saudiyya.
Masana sun ce wannan lamari ya haifar da ƙarin damuwa a kasuwar makamashi, inda farashin danyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 3.4% zuwa dala 94.07 kan kowace ganga, yayin da West Texas Intermediate (WTI) ya tashi da 3.0% zuwa dala 86.83.
A kasuwannin hannayen jari kuwa, kasuwar S&P 500 ta ragu da 0.1%, yayin da Nasdaq ya faɗi da 0.6%, sakamakon faduwar darajar manyan kamfanonin fasaha da ke zuba jari a fannin basirar wucin gadi (AI).
Masana kasuwanci sun bayyana cewa masu zuba jari na ci gaba da sa ido kan rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma sakamakon kasuwancin manyan kamfanonin fasaha, saboda waɗannan abubuwa na iya ƙara tasiri ga tattalin arzikin duniya da kasuwannin kuɗi.
