Tsohon ɗan wasan tsakiya na Super Eagles, Seyi Olofinjana, ya bayyana baƙin cikinsa kan yadda aka cire shi daga jerin ‘yan wasan Najeriya da suka halarci Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta shekarar 2010, duk da irin gudunmawar da ya bayar wajen samun tikitin zuwa gasar.
Olofinjana, wanda ya buga wa Najeriya wasanni 48 tsakanin shekarar 2000 zuwa 2011, ya ce har zuwa yau babu wanda ya sanar da shi dalilin da ya sa ba a zaɓe shi ba.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin PlayZone Podcast, inda ya ce ya buga dukkan wasannin neman gurbin shiga gasar, har ma ya jagoranci Super Eagles a matsayin kyaftin a wasu daga cikin wasannin.
A cewarsa, babu wani daga cikin masu horarwa ko Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (NFF) da ya kira ko ya yi masa bayani kan dalilin cire sunansa daga tawagar.
Olofinjana ya ce duk da cewa babu ɗan wasan da ke da tabbacin kasancewa cikin tawagar ƙasa, amma yana ganin ya kamata a ba shi bayani saboda irin gudunmawar da ya bayar.
Ya ƙara da cewa sanya rigar Najeriya koyaushe abin alfahari ne a gare shi, yana mai cewa duk lokacin da yake wakiltar ƙasar, yana yin hakan ne da cikakken kishin ƙasa da alfahari.
