Gwamnatin Jihar Oyo ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an sako dalibai da malamai da aka sace yayin harin da ‘yan bindiga suka kai makarantu uku a karamar hukumar Oriire ta jihar.
Mai bai wa gwamna Shawara kan Tsaro, Abayomi Fagbenro, ya bayyana cewa har zuwa safiyar Alhamis babu wani sahihin bayani da ke nuna an sako wadanda aka sace.
A cewarsa, rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne.
An kai harin ne a yankin Ahoro-Esinle/Yawota da ke Ogbomoso, inda aka kashe mutum biyu tare da sace kusan malamai da dalibai 30 daga makarantu uku.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin sakonnin da ke yawo sun yi ikirarin cewa an sako wadanda aka sace, yayin da wasu kuma suka bayyana labarin a matsayin karya.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Olayinka Ayanlade, ya ce shi ma bai samu wani rahoto na sakin wadanda aka sace ba.
Ya kara da cewa jami’an tsaro suna ci gaba da kokarin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.
Bayan harin, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu, ya tura karin jami’an bincike daga hedikwatar rundunar da ke Abuja domin taimakawa wajen ceto daliban da malaman.
Haka kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bukaci jami’an tsaro su gudanar da aikin ceto cikin kwarewa da gaggawa.
A gefe guda, Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun samu tuntubar masu garkuwar kuma ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wadanda aka sace.
Gwamna Seyi Makinde ya tabbatar da cewa gwamnati tana aiki tukuru domin ganin an sako duk wadanda aka yi garkuwa da su lafiya.
