Daraktan fasaha na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), Austin Eguavoen, ya bayyana cewa Super Eagles ba za su samu hanya mai sauki ba a rukuni na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta AFCON 2027.
An hada Najeriya a rukuni na L tare da Tanzania, Madagascar da Guinea-Bissau bayan gudanar da jadawalin gasar a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kasashe 48 ne aka raba zuwa rukuni 12, inda kasashe biyu mafi kyau daga kowanne rukuni za su samu gurbin shiga gasar da za a gudanar tsakanin watan Yuni da Yuli na shekarar 2027.
Da yake magana a Abuja ranar Alhamis, Eguavoen ya ce mutane da dama suna ganin Najeriya ta samu rukuni mai sauki, amma a ganinsa hakan ba gaskiya ba ne.
“Akwai masu tunanin rukuni ne mai sauki, amma ni ban dauke shi haka ba.
“Duk da tarihin Super Eagles da yadda muka taka rawar gani a AFCON din da ta gabata, dole ne mu kasance cikin shiri sosai.
“Ya kamata mu rika daukar wasa daya bayan daya,” in ji shi.
Eguavoen ya tuna yadda Guinea-Bissau ta ba Najeriya wahala a baya, yana mai cewa kungiyar ba karamar kungiya ba ce.
“Na tuna lokacin da muka hadu da Guinea-Bissau sun ba mu wahala sosai.
“Hatta lokacin Jose Peseiro wasan ya kasance mai tsauri kafin daga baya muka samu nasara,” ya ce.
Ya kuma bayyana cewa Madagascar da Tanzania kungiyoyi ne da suka samu ci gaba sosai kuma ba za a raina su ba.
“Madagascar kungiyar ce mai kyau kuma tana samun ci gaba sosai.
“Tanzania ma ta nuna karfi lokacin da muka hadu da ita a AFCON da ta gabata,” in ji shi.
Sai dai ya ce yana da yakinin cewa Super Eagles za su iya samun gurbin shiga gasar idan suka ci gaba da mayar da hanka8li da kokari.
