Dan kasuwa Richard Akinaka ya zama dan takarar jam’iyyar PDP na kujerar Sanatan Bayelsa ta Tsakiya gabanin babban zaben shekarar 2027.
An ayyana Akinaka a ranar Alhamis a matsayin dan takara daya tilo a cibiyar tattara sakamakon zaben fidda gwani da aka gudanar a makarantar firamare ta St. Peter’s da ke Yenagoa.
Mataimakin shugaban PDP na yankin sanatocin da kuma jami’in tattara sakamako, Mista Bidi Weris, ne ya sanar da nasararsa bayan kammala zaben fidda gwani a mazabu daban-daban na yankin.
Da yake jawabi bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Akinaka ya gode wa shugabannin jam’iyya, magoya baya da masu ruwa da tsaki bisa amincewar da suka nuna masa, yana mai bayyana takararsa a matsayin “amintacciyar nauyi.”
“Mutanenmu sun dade suna jiran cigaba da wakilci nagari, amma shekaru da dama sun wuce cikin rashin ci gaba da rashin wakilci mai kyau. Wannan zamani ya zo karshe yanzu.
“Yayin da muke shirin babban zabe, sakona ga al’umma shi ne sakon fata, kwarin gwiwa da cikakken alkawarin aiki,” in ji Akinaka.
Ya kuma yi alkawarin cewa manufarsa ita ce kawo ci gaba da anfani ga al’ummar yankinsa ba wai anfani na kashin kai ba.
Akinaka ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa PDP za ta yi aiki tare domin samun nasara a babban zaben shekarar 2027.
Nasarar tasa ta tabbatar da shi a matsayin dan takarar PDP na Sanatan Bayelsa ta Tsakiya a zaben 2027.
