Shahararren ɗan wasan barkwanci kuma mai yin satira a kafafen sada zumunta, Kevin Chinedu, wanda aka fi sani da “Governor Amuneke”, ya bayyana dalilinsa na ƙin karɓar tayin zama jakadan matasa na Hukumar Zaɓe ta Kasa Independent National Electoral Commission (INEC).
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Amuneke ya ce da farko ya ji farin ciki matuƙa da jin cewa an zaɓe shi don wannan matsayi, yana mai cewa ya ɗauki hakan a matsayin babban ci gaba a rayuwarsa.
“Na yi farin ciki sosai”
Ya ce labarin nadin ya sa shi jin alfahari sosai saboda irin gwagwarmayar da ya sha kafin ya zama sananne a fannin nishaɗi da satira.
Sai dai daga baya, ya ce farin cikin ya koma damuwa bayan ya fahimci wasu sharuɗɗa da ke tattare da aikin.
Batun ‘yancin suka
Amuneke ya bayyana cewa ya tambaya ko zai ci gaba da sukar INEC idan ya karɓi mukamin, sai aka ce masa zai iya yin wayar da kai kan zaɓe da rajistar katin zaɓe, amma ba zai halatta ya soki hukumar kai tsaye ba.
Ya ce wannan sharadi ya sa ya fara tunani, domin yawancin aikinsa ya ta’allaka ne kan sukar gwamnati da hukumomi domin inganta su.
Dalilin kin amincewa
Ya ce:
“Idan na karɓi wannan aiki, zan rasa ‘yancin da nake da shi na faɗin gaskiya. Wannan ya saba da manufar da nake da ita.”
Ya ƙara da cewa muryarsa ta ginu ne kan matsalolin jama’a da kuma matsalolin mulki a Afirka.
Sakon ga masu kirkira
Amuneke ya kuma yi kira ga sauran masu kirkirar abun ciki da su riƙe gaskiya da ‘yancinsu, ba tare da sun sayar da murya saboda mukami ko kudi ba.
