Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) reshen jihar Bauchi ta sake jaddada goyon bayanta ga Alhaji Shehu Musa Gabam a matsayin halastaccen Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, biyo bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 27 ga Maris, 2026, wanda ya soke ikirarin bangaren Sadiq Gombe.
A cikin sanarwar da shugaban SDP na jihar Bauchi, Hon. Nairy Husaini, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Bauchi, jam’iyyar ta bayyana cewa ba ta amince da duk wani bangare ko mutum da ke ikirarin wakiltar jam’iyyar ba tare da sahihancin doka ba.
Sanarwar ta ce hukuncin kotu ya tabbatar da cewa Shehu Musa Gabam ne halastaccen shugaban SDP, sannan kuma bayanan da hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta sabunta sun tabbatar da hakan.
SDP reshen Bauchi ta kuma yi watsi da bangaren Sadiq Gombe, inda ta bayyana cewa ba shi da wani ikon doka na wakiltar jam’iyyar ko ɗaukar kowane mataki a madadin ta.
