Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Faransa da ake kira Avocats Sans Frontières France (Lawyers Without Borders) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya da su tabbatar da an yi bincike na gaskiya da kuma gurfanar da wani jami’in ‘yan sanda, ASP Nuhu Usman, bisa zargin kashe wani matashi mai shekara 28, Mene Ogidi, ba bisa ka’ida ba.
A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba, wacce Country Director, Angela Uwandu-Uzoma-Iwuchukwu ta sa hannu, kungiyar ta ce ta yi Allah-wadai da abin da ta kira “kisan gilla ba tare da shari’a ba” da aka ce ya faru a Effurun, Jihar Delta, ranar 26 ga Afrilu, 2026.
Rahotanni da kuma wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta sun nuna cewa jami’in ‘yan sandan da ke aiki a Ofishin Yankin Effurun ne ya harbe wanda ake zargi.
Kungiyar ta ce wannan kisan ya nuna rugujewar tsarin doka da oda, kuma ya saba da ‘yancin rayuwa da Sashe na 33 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.
Ta kuma bayyana cewa hakan ya keta ka’idar rashin laifi har sai an tabbatar da laifin mutum a kotu, wacce Sashe na 36 na kundin tsarin mulki ya tanada.
Haka kuma, kungiyar ta ce kisan ya sabawa Dokar Aikin ‘Yan Sanda ta Najeriya (Police Order 237) wacce ke hana amfani da bindiga sai idan rayuwa na cikin hadari mai tsanani.
ASF France ta ce abin ya sabawa dokokin kasa da kasa kamar:
African Charter on Human and Peoples’ Rights
International Covenant on Civil and Political Rights (ICCPR)
Dukkan wadannan suna hana kisan da ba bisa ka’ida ba daga jami’an gwamnati.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa bidiyon da ake yadawa ya nuna cewa wanda aka kashe yana daure da hannu da ƙafa, kuma ba ya da wata barazana lokacin da aka harbe shi.
Duk da cewa an kama jami’in da ake zargi, kungiyar ta ce hakan bai isa ba, domin dole ne a kai shi kotu domin yanke hukunci na gaskiya.
A karshe, kungiyar ta gargadi cewa irin wadannan kisan-kashen da ba bisa doka ba na lalata amincewar jama’a ga gwamnati da kuma karya tsarin dimokuradiyya, kuma za su ci gaba da sa ido kan shari’ar har sai an tabbatar da adalci.