Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta bayyana cikakken goyon bayanta ga kiran Gwamna Seyi Makinde na a gudanar da bincike mai zaman kansa ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) kan sace ɗalibai da malamansu da aka yi a ƙaramar hukumar Oriire.
Majalisar ta ce irin wannan bincike zai taimaka wajen gano hakikanin abin da ya faru, ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya, da kuma samar da hanyoyin da za su hana sake aukuwar irin wannan hari a makarantu.
A cikin sanarwar da Ofishin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin, ya fitar, an taya gwamnatin jihar da al’ummar Oyo murnar nasarar ceto ɗaliban da malamansu da aka sace.
Majalisar ta jaddada cewa kiran Makinde ba suka ba ne ga Gwamnatin Tarayya ko hukumomin tsaro, illa wata hanya ce ta ƙara inganta gaskiya, haɗin gwiwa da nemo hanyoyin da za su ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.
Ta kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu, rundunar sojoji, jami’an leƙen asiri, ‘yan sanda, Amotekun da sauran jami’an tsaro bisa rawar da suka taka wajen ceto waɗanda aka sace.
Majalisar ta ƙara da cewa hare-haren ta’addanci da sace ɗalibai sun zama matsala mai wuce iyakokin ƙasa, don haka haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa na da muhimmanci wajen samar da ingantattun hanyoyin magance matsalar.
A ƙarshe, ta yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya su goyi bayan duk wani shiri da zai ƙara ƙarfafa tsaro, kare makarantu da tabbatar da lafiyar yara daga irin waɗannan hare-hare a nan gaba.
