Ɗan takarar gwamnan Jihar Osun na jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya yi watsi da kiran da Gwamna Ademola Adeleke ya yi ga Hukumar Diflomasiyyar Birtaniya (British High Commission) na hana wasu manyan jiga-jigan APC shiga ƙasar Birtaniya, yana mai bayyana buƙatar a matsayin “abin dariya.”
Oyebamiji ya ce jam’iyyar APC ta rasa mambobi da dama sakamakon rikicin siyasa a jihar, yana zargin cewa wasu daga cikin waɗannan hare-haren an aikata su ne daga mambobin jam’iyyar da ke mulki. Ya ƙara da cewa irin waɗannan lamuran sun faru tun lokacin zaɓen gwamna na shekarar 2022, kuma an kai rahotonsu ga jami’an tsaro, yayin da wasu shari’o’in ke gaban kotu.
Ya kuma ce APC ba ta taɓa amfani da irin waɗannan abubuwa wajen siyasantar da al’amura ba, sai dai ta ba hukumomin tsaro haɗin kai domin gudanar da bincike.
Dangane da kiran Adeleke na hana shugabannin APC biza, Oyebamiji ya ce idan akwai wata jam’iyya da za ta nemi irin wannan mataki, to APC ce ta fi cancanta bisa abin da ta ce ta fuskanta.
A nasa ɓangaren, Babban Mai Ba da Shawara kan Harkokin Siyasa na British High Commission, Wale Adebajo, ya bayyana cewa ziyarar da suka kai na daga cikin tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da zaɓen gwamna na Osun cikin lumana da adalci.
A baya dai, Gwamna Ademola Adeleke ya buƙaci a kakaba takunkumin tattalin arziki da hana wasu shugabannin APC biza, yana mai cewa kalamansu da ayyukansu sun ƙara rura wutar rikicin siyasa a jihar.
