Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar ambaliya, inda ta fara sa ido da tantance yankunan da ambaliya ta shafa a faɗin ƙasar nan, tare da shirin tattara sunayen dukkan garuruwa da al’ummomin da bala’in ya shafa a shekarar 2026 domin gudanar da ayyukan farfaɗowa bayan iftila’in.
Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin dabarun inganta hasashen ambaliya, bayar da gargaɗin wuri, da kuma rage asarar rayuka, dukiyoyi da muhimman ababen more rayuwa.
Ma’aikatar ta ce tana ci gaba da fitar da hasashen ambaliya na mako-mako ga Hukumomin Ba da Agajin Gaggawa na Jihohi (SEMAs), sauran hukumomin gwamnati, da mazauna yankunan da ke cikin haɗari domin su ɗauki matakan kariya tun kafin ambaliyar ta afku.
Haka kuma, an tura ƙungiyar Flood Vanguard Team zuwa yankunan da ambaliya ta shafa domin tantance girman barna tare da tattara sahihan bayanai daga hukumomi da kafafen yaɗa labarai.
Bisa ga ma’aikatar, bayanan da aka tattara za su taimaka wajen gano yankunan da suka fi buƙatar ayyukan gina kariya da sauran matakan fasaha a ƙarƙashin kasafin kuɗin gwamnati.
Ma’aikatar ta kuma tabbatar da cewa za a rubuta tare da wallafa jerin dukkan al’ummomin da ambaliya ta shafa a shekarar 2026, domin sauƙaƙa shirye-shiryen gyare-gyare da sake gina yankunan da bala’in ya lalata.
