Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su fara karanta dokokin da Majalisar Tarayya ke zartarwa kafin su soki ayyukan ‘yan majalisa.
Yayin ƙaddamar da National Assembly Open Week 2026 a Abuja, Akpabio ya ce yawancin suka da ake yi wa majalisar suna samo asali ne daga rashin fahimtar yadda ake tsara da zartar da dokoki. Ya jaddada cewa majalisa tana yin dokokin da za su amfani al’ummomi na tsawon lokaci, ba don amfanin ‘yan siyasa kawai ba.
Har ila yau, ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan sauye-sauyen tattalin arziki da kuma ƙoƙarin da take yi wajen inganta tsaro, musamman ceto ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo.
A nasa bangaren, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana cewa Majalisar ta karɓi kudurori 2,747 cikin shekaru uku, ta amince da 363, yayin da Shugaban Ƙasa ya sanya hannu kan 72 daga cikinsu. Ya kuma sanar da cewa za a janye tsohon kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin a ba da fifiko ga sabon kudirin da Shugaba Tinubu ya gabatar.
Sai dai ƙungiyar PLAC ta tunatar da majalisar cewa har yanzu ‘yan Najeriya na sa ran ganin ƙarin gaskiya, cikakken sa ido kan ayyukan gwamnati, da kuma dokokin da za su inganta rayuwar al’umma.
