Kungiyar Federation of Informal Workers Organizations of Nigeria (FIWON) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki batun tallafin jin dadin al’umma a matsayin wani muhimmin bangare na yaki da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar domin bikin Ranar Dimokuradiyya ta 12 ga Yuni, ta bayyana cewa karuwar talauci, rashin aikin yi da kuma rashin kulawa ga talakawa na daga cikin manyan abubuwan da ke kara haddasa satar mutane da sauran laifuka a Najeriya.
Babban Sakataren kungiyar, Kwamared Gbenga Komolafe, ya ce duk da cewa ranar 12 ga Yuni alama ce ta dimokuradiyya, har yanzu mafi yawan ‘yan Najeriya musamman masu sana’o’in hannu da ke bangaren tattalin arziki na yau da kullum ba su amfana da ribar dimokuradiyya ba.
Kungiyar ta nuna damuwa kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da sace-sacen mutane a sassan kasar nan, tana mai cewa matsalar tsaro ba za ta rabu da matsin tattalin arziki da ke addabar miliyoyin jama’a ba.
FIWON ta ce sama da kashi 93 cikin 100 na ma’aikatan Najeriya na aiki ne a bangaren da ba na gwamnati ba, amma har yanzu suna fama da rashin wutar lantarki, tsadar rayuwa, rashin ingantaccen kiwon lafiya da sauran muhimman tallafi.
Kungiyar ta kuma yi nuni da sace dalibai da malamai a wata makaranta da ke Jihar Oyo, tana mai cewa hakan wata alama ce ta yadda matsalolin zamantakewa da tattalin arziki ke kara haddasa rashin tsaro.
A cewar kungiyar, matasa da dama da ba su da aikin yi ko tallafin gwamnati suna fadawa hannun masu aikata laifuka saboda neman mafita ta rayuwa.
FIWON ta bukaci gwamnati ta kara fadada tsarin inshorar lafiya da fansho ga ma’aikatan bangaren sana’o’in hannu, tare da samar da karin ayyukan yi da horas da matasa sana’o’i.
Haka kuma ta yi kira da a samar da kariya ga makarantu da al’ummomin da ke fuskantar barazanar hare-hare domin tabbatar da cewa yara na samun ilimi cikin kwanciyar hankali.
Kungiyar ta jaddada cewa magance matsalar rashin tsaro ba ta ta’allaka ga amfani da jami’an tsaro kadai ba, sai an hada da samar da adalci, ayyukan yi da kuma tallafin rayuwa ga talakawan Najeriya.
“Dimokuradiyya ta gaskiya ba wai gudanar da zabe kadai ba ce, ana auna ta ne da yadda rayuwar jama’a ke inganta. Idan yara ana sace su, ma’aikata ba sa iya samun lafiya, tsofaffi kuma ba su da tallafi, to dimokuradiyya ta gaza,” in ji kungiyar.
