Kwamitin Kula da Asusun Jama’a (PAC) na Majalisar Wakilai ya samu nasarar kwato Naira miliyan 521.76 na harajin VAT da Babban Bankin Najeriya (CBN) bai tura wa gwamnatin tarayya ba, a wani bangare na binciken da yake yi kan gibin kudaden shiga da bashin da wasu hukumomi ke bin gwamnati.
Kwamitin ya gano cewa CBN bai remita VAT da ya kai N521,765,134.17 ba daga kudaden da aka samu ta hanyar mu’amalolin Remita tsakanin watan Nuwamban 2018 zuwa Afrilun 2024.
Bayan umarnin kwamitin, CBN ya tabbatar a wata wasika mai kwanan wata 7 ga Mayu, 2026 cewa ya bi umarnin tare da mayar da cikakken kudin cikin asusun gwamnatin tarayya.
Shugaban kwamitin, Hon. Bamidele Salam, ya ce wannan nasara ta nuna muhimmancin sa ido da Majalisar Dokoki ke yi wajen kare dukiyar jama’a da tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da kudaden gwamnati.
Ya kuma tabbatar da cewa kwamitin zai ci gaba da kokarin kwato duk wasu kudaden da ake bin gwamnatin tarayya tare da dakile duk wata hanyar da ke haifar da asarar kudaden shiga.
Kwamitin ya kara bayyana cewa har yanzu yana ci gaba da tattaunawa da CBN kan wasu kudade da suka hada da N954.30 miliyan na kudaden da ba a mayar ba da kuma ribar N2.32 biliyan, wanda jimillar su ta kai N3.28 biliyan.
Haka kuma, ana ci gaba da neman dawo da N8.99 biliyan na kudaden TSA da ba a mayar ba tare da ribar N20.72 biliyan, wanda ya kai jimillar bashin N29.72 biliyan.
Ana sa ran kwamitin zai ci gaba da sauraron karar a ranar Litinin, 8 ga Yuni, 2026, a harabar Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Abuja.
