Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta kara zage damtse wajen magance matsalolin tattalin arziki, inganta tsaro da kuma ceto mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
Sakon shugaban kasar ya fito ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, yayin taron addu’ar hadin gwiwar Kiristoci da aka gudanar a Abuja domin bikin Ranar Dimokuradiyya ta 2026.
Akume ya ce gwamnatin Tinubu ta san irin kalubalen da al’umma ke fuskanta, musamman matsin tattalin arziki, hare-haren ’yan ta’adda, garkuwa da mutane da kuma korar jama’a daga muhallansu.
Ya bayyana cewa gwamnati na aiki tukuru domin rage wadannan matsaloli tare da tabbatar da cewa dimokuradiyya ta kawo ci gaba ga rayuwar talakawa.
Dangane da tsaro, Akume ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar masu aikata laifuka, yana mai tabbatar da cewa ana kara karfafa jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya, musamman matasa, da su guji tashin hankali, yada labaran karya da kalaman da ka iya haddasa rabuwar kai yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027.
Sakataren ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa.
