Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya bayyana damuwarsa kan karuwar hare-haren sace mutane yayin da kasar ke kara kusantar babban zaben shekarar 2027, yana mai gargadin cewa bai kamata a bari matsalar tsaro ta kara kamari ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron ibada da aka gudanar a LoveWorld City (Christ Embassy) da ke Benin City, inda ya yi kira da a kara addu’o’i domin kawo karshen sace-sacen mutane, rikicin kungiyoyin asiri da sauran matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
Okpebholo ya ce karuwar sace-sacen mutane, musamman a lokacin da harkokin siyasa ke fara zafi gabanin zabe, abin damuwa ne da ke bukatar kulawa ta gaggawa daga kowa da kowa.
Ya ce, “Wannan kasa ba mallakin masu garkuwa da mutane ba ce. Bai kamata wani mutum ko wata kungiya ta rike kasar a matsayin garkuwa domin cimma muradunta na siyasa ko na kashin kai ba.”
Ya kara da cewa, “Yayin da zabe ke kara matsowa, matsalar sace mutane na kara kamari. Amma da addu’o’in bayin Allah da hadin kan jama’a, muna da yakinin za a shawo kan wadannan kalubale.”
Gwamnan ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, tsaro da farfado da tattalin arziki, yana mai jaddada cewa hadin kai da daukar alhakin kasa tare ne za su taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta.
Haka kuma ya yi kira da a yi wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu addu’a domin Allah Ya ba shi hikima da karfin jagorantar kasar yadda ya kamata.
A cewarsa, magance matsalolin tsaro da wahalhalun tattalin arziki na bukatar hadin gwiwar gwamnati, jama’a da kuma taimakon Allah.
A nasa jawabin, Fasto Moses Olayemi wanda ya jagoranci taron ibadar ya gudanar da addu’o’i na musamman domin Najeriya, shugabanninta da al’ummominta, yana rokon Allah Ya kawo zaman lafiya, kariya da bunkasar tattalin arziki.
Olayemi ya kuma yaba wa Gwamna Okpebholo kan ayyukan ci gaba da yake gudanarwa a Jihar Edo, musamman a bangaren tituna, yana mai cewa mazauna jihar sun fara ganin tasirin wadannan ayyuka.
