Wasu magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Bauchi sun yi watsi da zargin yunkurin kakaba dan takarar gwamna kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar, inda suka bukaci a gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci.
Masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun bayyana matsayinsu ne a ranar Alhamis yayin wata ziyara da suka kai otal din da aka sauke kwamitin zaben APC domin neman karin bayani kan jinkirta zaben fidda gwani na gwamna.
Wani jigo a APC, Musa Buba Mohammed wanda aka fi sani da “Civilian General,” ya ce mambobin jam’iyyar ba za su amince da kokarin wasu tsirarun mutane na kakaba musu dan takara ba.
Ya ce dimokuradiyya dole ta kasance bisa ra’ayin mambobin jam’iyya ba wai anfani na wasu kalilan ba.
“Mun zo ne domin bayyana korafinmu saboda dimokuradiyya gwamnati ce ta jama’a, daga jama’a kuma domin jama’a, ba gwamnati ta wasu tsiraru ba,” in ji shi.
Mohammed ya ce magoya bayan APC a Bauchi suna bukatar zabe mai gaskiya da adalci wanda zai samar da dan takarar da mambobin jam’iyya da al’umma za su amince da shi.
Ya kara da cewa duk da an dage zaben daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, har yanzu suna da fatan za a gudanar da zaben cikin gaskiya.
A cewarsa, magoya bayan jam’iyyar na da yakinin cewa dan takara Nura Manu Soro zai samu nasara idan aka samar da yanayi mai adalci ga kowa.
Ya kuma yi kira ga shugabannin APC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da su tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaben.
Mohammed ya ce dage zabukan fidda gwani a Bauchi da Kwara ya jefa shakku a zukatan mambobin jam’iyyar, inda mutane da dama ke zargin akwai yunkurin magudi.
“Me yasa aka dage zaben? Dole akwai wani dalili a bayan hakan. Sauran jihohi sun gudanar da zabensu amma Bauchi da Kwara aka dage. Wannan ne ya sa mutane ke fara zargin akwai wata manufa,” ya bayyana.
Ya kara da cewa mambobin jam’iyyar sun samu bayanin dage zaben amma sun dage cewa sai an gudanar da sahihin zabe ne kawai za a ci gaba da samun amincewa da jam’iyyar.
Mohammed ya kuma bayyana cewa APC dole ta kare tsarin dimokuradiyya a cikinta, yana mai cewa Shugaba Tinubu ma ta hanyar zabe ya samu tikiti ba ta hanyar maslaha ba.
“Shugaban kasa ta hanyar kuri’a ya samu nasara, ba ta hanyar yarjejeniya ba. Wannan irin tsarin dimokuradiyya muke bukata a Bauchi,” in ji shi.
Shi ma wani mamba a jam’iyyar, Kwamared Abdul’Aziz Nasrullah, ya bukaci a gudanar da sahihin tsari, yana mai cewa Bauchi na bukatar nagartattun ‘yan takara masu wakiltar muradun jama’a.
Ya yi gargadin cewa kakaba dan takara na iya haddasa rabuwar kai a cikin jam’iyyar.
Dukkan bangarorin biyu sun jaddada biyayyarsu ga APC amma suka ce dole ne a tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana a zaben fidda gwani na gwamna a jihar Bauchi.
