Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Yobe sun tabbatar da Sanata Ibrahim Mohammed Bomai a matsayin dan takarar hadin kai na kujerar Sanatan Yobe ta Kudu gabanin zaben shekarar 2027.
An tabbatar da hakan ne bayan tattaunawa da shawarwari da shugabannin jam’iyyar, dattawa da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar domin tabbatar da hadin kai a cikin APC a jihar.
An gudanar da taron amincewar ne a dakin taro na Federal College of Education da ke Potiskum, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Buba Mashio, tare da halartar manyan jiga-jigan APC, kungiyoyin matasa da magoya bayan jam’iyyar daga sassan mazabar.
Jami’an jam’iyyar sun bayyana cewa an dauki matakin amincewa da Bomai ne bayan doguwar tattaunawa domin kauce wa rikicin cikin gida tare da tabbatar da zaman lafiya kafin babban zabe.
Tun farko dai Sanata Bomai ya janye daga takarar gwamnan jihar Yobe kafin daga bisani ya zama zabin hadin kai na kujerar Sanata.
Da yake jawabi bayan tabbatar da shi, Bomai ya gode wa shugabanni da magoya bayan jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna masa, yana mai alkawarin ci gaba da yi wa al’ummar Yobe ta Kudu aiki tukuru.
“Ina mika godiyata ga shugabannin jam’iyya, dattawa da dukkan magoya bayanmu bisa irin goyon bayan da suka ba ni. Zan ci gaba da kare muradun al’ummar Yobe ta Kudu yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya kuma yabawa sauran ‘yan takara da magoya bayan jam’iyyar bisa yadda suka rungumi zaman lafiya da hadin kai a duk lokacin tattaunawar.
Masana harkokin siyasa a jihar sun bayyana cewa fitowar Bomai a matsayin dan takarar hadin kai na iya rage rikice-rikicen cikin gida a APC, musamman ganin cewa yankin Yobe ta Kudu na daga cikin yankunan da jam’iyyar ke da karfi sosai.
Idan aka sake zabensa a 2027, Bomai zai koma majalisar dattawa karo na uku a jere, lamarin da zai kafa sabon tarihi a mazabar Yobe ta Kudu.
