Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (Nigeria Immigration Service – NIS) ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da tsarin neman fasfo da biyan kudinsa, tana mai cewa labaran ba su da tushe kuma suna iya rikita jama’a.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, hukumar ta jaddada cewa tsarin neman fasfo na dijital yana da tsaro kuma ana gudanar da shi ne kawai ta hanyar shafin hukuma.
Ta ce:
“Hukumar NIS na gudanar da tsarin neman fasfo mai tsaro, gaskiya da amincewar gwamnati, wanda ake shiga shi ne kawai ta shafin hukuma.”
Hukumar ta kara da cewa shafin hukuma shi ne kadai hanyar da aka amince da ita wajen dukkan harkokin neman fasfo da biyan kudi, ko a Najeriya ko mazauna kasashen waje.
Ta gargadi jama’a da cewa duk wani shafi da ba na hukuma ba ya kamata a dauke shi a matsayin zamba.
NIS ta kuma karyata ikirarin da ke cewa wata kungiya ta addini ko wata hukuma mai zaman kanta tana da hannu a tsarin biyan kudin fasfo.
“Babu wani lokaci da hukumar ta bai wa wata kungiya ta addini, ko kamfani mai zaman kansa, ko wani mutum izinin shiga tsakani ko karɓar kudade a madadinta,” in ji sanarwar.
Hukumar ta bayyana cewa tana bincike kan asalin wannan labarin na bogi tare da gargadin daukar mataki kan masu yada shi.
“Mun fara bincike kan wannan ikirari, kuma za mu dauki mataki kan duk wanda aka samu da hannu,” in ji NIS.
A karshe, hukumar ta bukaci jama’a da su rika amfani da hanyoyin hukuma kawai tare da kauce wa duk wani shafi ko wakili mara izini wajen neman fasfo
