Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dauki tare da tura sama da ma’aikatan jinya da ungozoma 1,500 zuwa yankunan karkara domin inganta harkokin kiwon lafiya, musamman a wuraren da ba su da isassun ma’aikata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar lafiya karo na takwas da aka gudanar a jihar.
A cewarsa, gwamnatin ta bullo da tsarin aikin dole na shekaru biyu a yankunan karkara domin tabbatar da rabon ma’aikatan lafiya cikin adalci a fadin jihar.
“A karkashin manufofinmu na 9-SMART, mun kafa tsarin aikin dole na shekaru biyu a karkara domin tabbatar da cewa an raba ma’aikatan lafiya yadda ya kamata, musamman a yankunan da ke fama da karancin ma’aikata,” in ji shi.
Gwamnan yakara dacew “Mun dauki sama da ma’aikatan jinya da ungozoma 1,500 tare da samar musu da alawus domin karfafa musu gwiwar aiki a karkara.”
Gwamnan ya ce wannan mataki zai taimaka wajen magance matsalar karancin kwararrun ma’aikatan lafiya a yankunan karkara, wadda ta dade tana hana jama’a samun ingantaccen kiwon lafiya.
Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati na shirin daukar karin ma’aikatan lafiyar al’umma 2,400 tare da hadin gwiwar hukumomin lafiya na kasa.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar na sane da gibin da ake da shi a bangaren ma’aikatan lafiya, musamman wajen kula da lafiyar mata da yara.
Bugu da kari, gwamnatin jihar ta hada gwiwa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo domin samar da kwararrun likitoci da horaswa ga cibiyoyin lafiya a jihar.
Sabbin ma’aikatan da aka dauka za su rika samun karin kaso 10 cikin 100 na alawus saboda aikin karkara domin kara musu kwarin gwiwa.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Faruk Abubakar, ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da kowa ya samu damar samun ingantaccen kiwon lafiya.
Masu ruwa da tsaki daga kungiyoyin ci gaba, ciki har da Asusun Kula da Yawan Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA), sun yabawa wannan tsari, suna masu cewa zai taimaka sosai wajen samar da kwararrun ma’aikatan lafiya a yankunan da ke da wahalar isa.
