Jagoran jam’iyyar ADC, ya soki gwamnatin Najeriya kan matsalar tsaro da kuma ci gaba da ƙarancin wutar lantarki a ƙasar, yana mai cewa alƙawuran da aka yi wa ‘yan Najeriya ba a cika su ba.
Ya tuna kalaman Shugaban ƙasa da ya taɓa cewa idan bai samar da wutar lantarki ba, a kada shi, yana mai cewa har yanzu matsalar wutar na ci gaba da zama babban ƙalubale a ƙasar.
Okonkwo ya ce matsalar rashin tsaro ita ce babbar matsalar Najeriya a halin yanzu, yana gargadin cewa ba tare da tsaro ba, sauran fannonin gwamnati ba za su yi tasiri ba.
Ya kuma yi zargin cewa hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro a Jihar Borno da sauran sassan ƙasar suna nuna girman matsalar rashin tsaro, yana cewa ta zama abin da ke faruwa kullum.
A cewarsa, “ba wai kawai babu tsaro ba ne, gwamnati ma ta kasa samar da shi yadda ya kamata,” yana mai cewa matsalar ta kai matakin da ba za a iya ci gaba da yin watsi da ita ba.
Okonkwo ya yi kira da a mayar da hankali kan tsaro domin tabbatar da ci gaban ƙasa, yana mai cewa babu wani ci gaba da zai yiwu idan babu tsaro.
