Babbar Kotun Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Halifa Usman Sheka hukuncin shekara 1 a gidan gyaran hali bayan ta same shi da laifin fashi da makami a Unguwar Gurun Gawa, Kumbotso.
Matashin ya kai hari kan wata mata mai suna Hadiza Abdulrazak a shagon ta, inda ya yi mata fashi da makami tare da jikkata ta a hannunta.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Musa Ahmad, ya ce shaidu sun tabbatar da laifin, sai dai kotun ta yi la’akari da cewa ya shafe kusan shekaru 3 a tsare kafin kammala shari’ar.