Kwamishinan tsaro na cikin gida, Dr. Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa harin ramuwar gayya ne, bayan al’ummar yankin sun kai farmaki kwanaki biyu da suka gabata inda suka kashe wasu daga cikin ƴan ta’addan tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin jihar ta ce ta tura karin jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
Gwamnati ta kuma yi ta’aziyya ga iyalan da abin ya shafa, tare da yabawa jarumtar al’ummar yankin wajen fuskantar ƴan ta’adda.
#Asrah24TV #BreakingNews #Katsina #Tsaro