A zaɓukan cike gurbin da aka yi a Najeriya a ƙarshen mako, ana ganin sakamakon sun zo da ba-zata, musamman ganin yadda duk da irin rawar ganin da babbar jam’iyya mai mulkin a ƙasar ta taka, wasu jam’iyyu sun samu nasara a jihohin da suke mulki.
An gudanar da zaɓukan ne domin maye gurbin zaɓaɓɓu 16 a sassa daban-daban na jihohin ƙasar 12, inda APC ta lashe mafi yawan kujeru.
Babban abin da ya ɗauki hankali a zaɓen shi ne irin rawar jam’iyyar ADC ta haɗakar manyan ƴansiyasar adawa ta ƙasar ta taka, inda wasu suka yi tunanin ba ta yi takaɓus ba a lokacin da ya kamata ta nuna ƙwanji.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ya ce ko kaɗan bai kamata a fara kwatanta ƙoƙarinsu da abin da ya faru a zaɓen ba, domin a cewarsa, yanzu suka fara shiri.