Rundunarw ’Yan sandan Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar Hukumar DSS da sauran jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin mai sayen kuri’u a jihar.
An kama shi ne a daren kafin zaɓen cike gurbi na yau, inda aka gano kuɗi har Naira miliyan 25,963,000 da ake zargin an tanada su domin sayen kuri’u.
Hukumomin tsaron sun ce bincike ya na ci gaba, tare da tabbatar da cewa za su kara tsaurara matakan tsaro domin ganin an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci ba tare da katsalandan ba.