Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da kafa sababbin jami’o’in tarayya, kwalejojin fasaha (polytechnics), da kwalejojin ilimi a fadin kasar nan na tsawon shekaru bakwai.
Gwamnatin ta ce wannan mataki na da nufin magance raguwar inganci da kuma matsalolin kayan aiki a bangaren ilimin gaba da sakandare na kasar.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana haka ga ‘yan jarida bayan taron majalisar zartarwa ta kasa (FEC) da aka gudanar a ranar Laraba, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.