Kwamishinan yansandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taro na musamman da masu ruwa da tsaki kan zabukan da za a gabatar.
Ya kuma ce duk mutumin da suka kama da makami ko shigo da wasu mutane daga wasu jihohin ko kananna hukumomin Kano zai dandana kudar sa.
Bakori ya kuma ja kunnan duk wanda yasan ba zabe zai ba daya guji zuwa yankunan da za a gudanar da zabukan dan kuwa idan suka kama mutum doka za tai aiki a kansa.