Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Asrah 24 TV
  • Education
  • Health
  • Podcast
  • Politics
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
Facebook X (Twitter) YouTube WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
ASRAH 24 MEDIA
Subscribe
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    CBN Ta Ce Sauye-Sauyen Tattalin Arziki Sun Kafa Tubalin Ci Gaba Da Daidaiton Arzikin Najeriya

    August 6, 2026

    KOTU TA SAMU MACE DA LAIFIN YUNKURIN KASHE ƳAR SHEKARA 9 BAYAN TA YAUDARE TA ZUWA DAJI

    June 26, 2026

    KOTU TA KI SAKIN SOWORE, TA DAGE YANKE HUKUNCI ZUWA 30 GA YUNI

    June 24, 2026

    Sarkin Ilorin Ya Taya Musulmi Murnar Sabuwar Shekarar Hijira, Ya Yi Kiran Hadin Kai

    June 16, 2026

    Hukumar Kula da Mahajjatan Kano Ta Kayyade 25 ga Agusta a Matsayin Ranar Ƙarshe ta Miƙa Fasfo

    August 8, 2026

    📰 Labarin Yanar Gizo (Hausa Version): Kaduna Pilgrims Board Ya Tabbatar An Yi Hadaya Ga Duk Masu Biyan Kuɗi

    June 9, 2026

    Najeriya Ta Fuskanci Limit na Visa zuwa Amurka – 3 Mako Kaɗai!

    July 9, 2025

    Gwamnatin Tarayya Tare da Faransa Za Su Inganta ICT a Jami’o’in Najeriya da Tallafin Naira Biliyan 38

    July 4, 2025

    Fabiyi Ya Bukaci A Yi Autopsy Kafin A Binne Jarumar

    August 10, 2026

    Hukumar Kula da Mahajjatan Kano Ta Kayyade 25 ga Agusta a Matsayin Ranar Ƙarshe ta Miƙa Fasfo

    August 8, 2026

    Baturen Spain Ya Zo Legas Neman Masu Damfarar Mahaifiyarsa Ta Soyayya

    August 8, 2026

    CBN Ta Ce Sauye-Sauyen Tattalin Arziki Sun Kafa Tubalin Ci Gaba Da Daidaiton Arzikin Najeriya

    August 6, 2026
  • Asrah 24 TV
  • Education

    Farfesa Oloyede Ya Ajiye Muƙaminsa a JAMB Bayan Shekaru 10, Ya Koma Koyarwa

    July 31, 2026

    Ɗalibin UNILAG Ya Lashe Gasar Huawei ta ICT ta Duniya a China

    July 31, 2026

    Yajin Aikin ASUU Ya Jefa Daliban Jami’ar AAUA Cikin Rashin Tabbas

    July 27, 2026

    Save the Children Ta Mara Wa Kaduna Baya Don Mayar Da Yara 100,000 Makaranta

    July 24, 2026

    ‘Yar Ministan Abuja Nyesom Wike Ta Samu Digirin Lauya A Birtaniya

    July 22, 2026
  • Health

    ICPC Ta Gurfanar da Likitan El-Rufai Kan Zargin Ƙirƙirar Rahoton Lafiya na Karya Domin Neman Beli

    July 20, 2026

    Masana Sun Yi Gargadin Cewa Gano Cutar Sarcoma Da Wuri Na Iya Taimakawa Wajen Ceto Rayuka

    July 16, 2026

    Kusan Kashi 45% Na Cutar Dementia Ana Iya Hana Ta Ta Hanyar Canza Salon Rayuwa

    July 15, 2026

    Yobe, Qatar Charity Sun Kaddamar da Shirin Kyauta na Duba Ido da Aikin Cataract

    July 15, 2026

    Shahararren Mai Binciken Abinci, Opeyemi Famakin, Ya Ba Da Labarin Yadda Aikin 9-zuwa-5 Ya Gina Rayuwarsa

    July 13, 2026
  • Podcast
  • Politics

    SERAP Ta Buƙaci ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa 19 Su Bayyana Kadarorinsu Gabanin Zaɓen 2027

    August 9, 2026

    APC Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan Kaduna Ya Nemi Kudancin Kaduna Su Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu Da Uba Sani

    August 8, 2026

    APGA Candidate Ya Janye Waɗa, Ya Goyi Bayan Oyebamiji Na APC

    August 8, 2026

    Uzodimma Ya Mayar Wa Davido Martani Kan Zaɓen Gwamnan Osun

    August 6, 2026

    Zaɓen 15 Ga Agusta Zai Isar Da Saƙo Ga APC – Gwamna Adeleke

    August 6, 2026
  • Sports

    Harry Kane Ya Lashe Kyautar European Golden Shoe Ta 2025/26

    August 10, 2026

    Kungiyoyin Premier League Na Gaggawar Kammala Sayayya Kafin Rufe Kasuwar ’Yan Wasa

    August 8, 2026

    Chelsea Ta Lallasa AC Milan 3-0, Ta Lashe Kofin Indonesia Super Cup

    August 8, 2026

    Kasashe 13 Sun Janye Goyon Bayan Infantino Gabanin Zaben Shugabancin FIFA na 2027

    August 8, 2026

    NANS Ta Bukaci ‘Yan Arewa Su Guji Siyasantar Da Gyaran Tsarin Fitar Da Fasfo

    August 6, 2026
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
ASRAH 24 MEDIA
Home » Gwamnatin Neja ta nemi sulhu da gidan rediyon Badeggi FM
News

Gwamnatin Neja ta nemi sulhu da gidan rediyon Badeggi FM

Asrah24 MediaBy Asrah24 MediaAugust 13, 20253 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp

IMG 2938Gwamnatin jihar Neja ta amince da sulhun bayan fage a maimakon shiga kotu da gidan rediyon Badeggi (90.1 FM Radio Station) – kafar yaɗa labarai mai zaman kansa da ke garin Minna – wanda gwamnan jihar Neja, Mohammed Bago, ya ba da umarnin rufewa.

Kafar yaɗa labaran ta shigar da gwamnatin jihar ƙara a gaban kotu kwanaki biyar bayan tilasta mata rufe gidan rediyon a ranar 5 ga Agusta ta hannun lauyanta mai suna, Philip Emmanuel.

A ranar Litinin, a lokacin zaman kotu kan shari’a mai lamba NSHCM/0296/2025 a gaban babbar kotun Minna mai lamba 4, inda lauyan gwamnati Jacob Usman ya sanar da cewa gwamnati tana son tattaunawa a wajen kotu domin sulhuntawa da gidan rediyon.

Usman ya bayyana wa kotun cewa ya tattauna da lauyan waɗanda suka shigar da ƙara domin warware matsalar saboda samun zaman lafiya albarkacin al’ummar jihar Neja.

Ya kuma bayyana wa kotun cewa ya riga ya sanar da mista Emmanuel cewa babban antoni-janar na jihar Neja ya amince ya warware matsalar a wajen kotu.

Mista Emmanuel daga baya ya tabbatar wa da ‘yan jarida cewa, “mun zaɓi ranar 3 ga Satumbar 2025 domin tattaunawa a wajen kotun.”

Mai shari’a, Mohammed Mohammed, a ranar 5 ga Agusta, ya amince da roƙon da mai shigar da ƙara gidan rediyon Badeggi Broadcasting Service Ltd, da manajin-daraktan Mohammed Badeggi.

A cikin hukuncin da ya yanke, mai shari’a Mohammed, ya dakatar da gwamnan jihar da antoni-janar da hukumar bunƙasa birane ta jihar daga ɗaukar mummunan mataki da ka iya shafar lasisin gidan rediyon da ginin gidan yaɗa labaran da ke harabar gidan NTA da ke saman dutsen Minna.

PREMIUM TIMES ta rawaito yadda gwamna Bago ya ba da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM saboda zargin ƙoƙarin haifar da husuma.

Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin zaman jiga-jigan jam’iyyar APC wanda aka yi a gidan gwamnati da ke Minna.

Ya kuma ce an ɗauki matakin ne saboda irin ayyukan da gidan rediyon ke yi wanda ya saɓa wa ƙa’ida.

Bago ya kuma zargi mamallakin gidan rediyon da ƙoƙarin tunzura al’umma a kan gwamnati inda ya buƙaci a soke lasisin gidan rediyon.

Gwamnan ya kuma ba wa kwamishinan tsaron cikin gida da rundunar ‘yan sanda umarnin rufe gidan rediyon.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama kamar SERAP da CJID sun yi Alla-wadai da matakin da gwamnan jihar ya ɗauka. Ƙungiyoyin sun kuma zargi gwamnan da ƙoƙarin murƙushe kafafen yaɗa labarai da tauye ‘yancin faɗar albarkacin baki a jihar.

Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp
Previous ArticleEFCC ta ba da belin tsohon gwamnan Sokoto Waziri Tambuwal da ta tsare
Next Article Gwamnatin Najeriya ta yi maraba da naɗin Maryam Bukar-Hassan a matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya

Related Posts

Fabiyi Ya Bukaci A Yi Autopsy Kafin A Binne Jarumar

August 10, 2026

Hukumar Kula da Mahajjatan Kano Ta Kayyade 25 ga Agusta a Matsayin Ranar Ƙarshe ta Miƙa Fasfo

August 8, 2026

Baturen Spain Ya Zo Legas Neman Masu Damfarar Mahaifiyarsa Ta Soyayya

August 8, 2026

CBN Ta Ce Sauye-Sauyen Tattalin Arziki Sun Kafa Tubalin Ci Gaba Da Daidaiton Arzikin Najeriya

August 6, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Fabiyi Ya Bukaci A Yi Autopsy Kafin A Binne Jarumar

August 10, 2026

Funke Akindele Ta Fitar Da Jaruman Sabon Fim Ɗinta ‘The Four’

August 10, 2026

Harry Kane Ya Lashe Kyautar European Golden Shoe Ta 2025/26

August 10, 2026

’Yan Sandan Kogi Sun Ƙara Ƙaimi Wajen Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Okene-Auchi

August 9, 2026

Algeria Da Morocco Sun Samu Tikitin Gasar Kofin Duniya Ta Mata ta 2027

August 9, 2026
Connect with us
  • Facebook
  • Twitter
  • YouTube
  • WhatsApp
  • Instagram
  • TikTok
Top Posts
Advertisement
© 2026 ASRAH 24 MEDIA. Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.