Majalisar tsaron Isra’ila ta amince da buƙatar firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu ta mamaye dukkan birnin Gaza, yankin da ke cikin yaƙi kusan shekara biyu a jere.
Ofishin firaministan Isra’ilan ya ce da wannan amincewa, dakarunsu za su karɓe iko a birnin Gaza, inda ɗaruruwan Falasdinawa ke rayuwa.
Wannan mataki wanda Mr Netanyahu ke jagoranta ya fuskanci turjiya a Isra’ila, domin kuwa ƴan’uwan mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su na ganin cewa za a jefa rayuwar ƴan’uwan nasu a cikin hatsari da Zarar an fara aiwatar da Shirin.
Akwai kuma fargabar cewa matakin zai buɗe sabuwar hanyar ci gaba da kisan Falasɗinawa fararen hula.