Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana haka ranar Juma’a yayin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar kula da gidajen yari na ƙasar, Sylvester Nwakuche, a ofishin INEC da ke Abuja.
Yakubu ya ce hukumar ta yi jerin ganawa da hukumar kula da gidajen yarin domin tsara yadda ɗaurarrun za su kaɗa ƙuri’ar tasu, ciki har da samun damar zuwa inda suke ɗaure domin ba su damar jefa ƙuri’a.
Haka kuma shugaban na INEC ya nemi ɗaukin majalisar dokokin ƙasar domin tabbatar da ƙudurin