Wata ɗalibar Najeriya, Maryam Lawal, ta kafa tarihi a Jami’ar Oxford dake Burtaniya bayan ta lashe lambar yabo ta “Best Graduating Student” a fannin Artificial Intelligence.
Maryam, ‘yar asalin jihar Kaduna, ta samu maki mafiya ɗaukaka daga cikin ɗalibai 312 a wannan fanni, wanda ya sa ta jawo hankalin manyan kamfanonin duniya kamar Google, Tesla da kuma Microsoft.
A wata hira da aka yi da ita bayan kammala karatu, Maryam ta ce:
> “Na tashi daga iyali mai talauci a Arewa, amma na dage da addu’a da karatu. Wannan nasara ta fi karfina – Allah ne ya yi.”
Gwamnatin Najeriya ta bayyana shirin karrama ta da lambar yabo ta kasa, yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta ce za ta bayar da tallafin gina cibiyar koyar da Artificial Intelligence a garinta.
