Hukumar kula da yanayi ta kasa NiMet, ta yi hasashen samun ruwan sama da cida daga yau Laraba zuwa jibi Juma’a a fadin kasar nan.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wani rahoto da ta fitar a daren jiya Talata a birnin tarayya Abuja, inda ta ce, jihohin Taraba da Kaduna da kuma Adamawa za su fuskanci wannan yanayi a yau Laraba.
Rahoton ya kara da cewa jihohin Kebbi da Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto sai Gombe da Bauchi da Benue da Kwara da Neja da Nasarawa da Birnin tarayya Abuja da kuma nan Kano, duk su ma za su fuskanci mamakon ruwan saman da kuma cida a tsakanin wadannan kwanaki.
Hukumar, ta kuma ja hankalin al’umma da su guji yin tukin ababen hawa a yayin da ake tafka ruwa, kana a kashe kayakkain lantarki daga jikin Soket tare da kaurace wa tsaya wa ko kuma fakewa a karkashin bishiyu.
Haka kuma, hukumar ta NiMet ta shawarci hukumomin lura da sifurin jiragen sama da su tabbatar da daukar matakan da suka dace.
