Gwamnatin jihar Kano ta ce daliban makarantun Furamare dana Sakandare za su tafi dan takaitaccen hutun bikin sallah babba mai zuwa daga ranar 4 ga watan da muke ciki na Yuni zuwa ranar Lahadi 15 ga watan, ga daliban dake makarantun kwana.
Haka zalika gwamnatin ta ce daliban dake makarantun jeka ka dawo kuma za su dawo a ranar Litinin 16 ga watan na Yuni.
Wannan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashin yada labarai na ma’aikatar Ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya fitar, inda ya yiwa Freedom Radio karin haske kanta.
Daraktan sashin yada labarai na ma’aikatar Ilimi Balarabe Abdullahi Kiru kenan.
