Majalisar Dattawan kasar nan ta amince da kafa kwamitin wucin gadi domin shirya taron ƙasa na kwana biyu kan matsalolin tsaro a birnin tarayya Abuja.
Taron na da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan ta hanyar haɗa kai da duk hukumomin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi – tare da sarakunan gargajiya da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin tsaro.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya amince da kudirin kuma ya umurci kwamatin wucin gadin da ya fara shirye-shiryen taron nan take.
Ana sa ran taron zai samar da mafita mai amfani da haɗin kai ga matsalolin da ke barazana ga zaman lafiyar kasa.
