Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya shiga tsakani a rikicin filaye tsakanin Jami’ar Bayero (BUK) da al’ummar Rimin Zakara don mayar da filin hannun jami’ar.
Tinubu, wanda Karamar Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, ta wakilta a bikin yaye daliban jami’ar karo na 39 a jiya Asabar, ya bukaci a mayar wa da BUK takardun mallakar filin. Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta ware kudade don gina shinge a kewayen jami’ar.
Haka nan, shugaban ya bukaci jami’o’i su rungumi nazari da bincike don samar da hanyoyin wutar lantarki mai zaman kanta, domin rage kudaden da ake kashewa wajen samar da wuta.
