Babbar kotun jihar Kano ta dage sauraron shari’ar da ke gudana kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da mai dakinsa, Hafsat Ganduje.
Baya ga Ganduje da matarsa, akwai karin mutane shida da ake tuhuma kan karkatar da kudaden al’umma a lokacin mulkinsa. Kotun ta saka ranar 15 ga watan nan don cigaba da shari’ar da sauraron hujjoji kan wasu batutuwan da ba a amince dasu ba a zaman baya.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje da laifuka takwas da suka hada da cin hanci, rashawa, da almundahana. Sauran wadanda ake zargi sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Sage General Enterprises Limited.
