Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad, ya ce abin takaici ne Najeriya tana fama da karancin abinci duk da albarkatun noma da take da su. Yayin da yake karɓar bakuncin jakadan Portugal, Paulo Martins, a fadar gwamnati, gwamnan ya jaddada cewa amfani da dabarun noma na zamani da zuba jari a fannin aikin gona zai taimaka wajen magance matsalar. Ya kuma bai wa jakadan tabbacin cewa Bauchi na da filayen noma masu kyau da suka dace da zuba hannun jari ba tare da matsalar cin hanci ko haraji mai yawa ba. A nasa bangaren, Paulo Martins ya ce Portugal na duba yiwuwar haɗin gwiwa da jihar Bauchi don inganta harkar noma.
Gwamna Bala Muhammad: Rashin Ishasshen Abinci a Nigeriya Abin Kunya Ne,
Previous ArticleHamas Ta Ce Maganganun Trump Na Iya Hana Cimma Tsagaita Wuta
Next Article Nageriya Ta Kama Matsayi Na 140 a Cin Hanci a 2024
Related Posts
Add A Comment
