Hafsan hafsoshin tsaron Nigeria, Christopher Musa, ya bayyana cewa dakarun soji sun kashe manyan kwamandojin da ke taimakawa fitaccen dan ta’adda, Bello Turji. Musa ya fadi hakan ne a Abuja ranar Juma’a.
A baya an yi jita-jitar cewa an kashe Turji yayin wani farmaki a Zamfara, amma daga bisani rundunar sojin ta karyata hakan. Duk da haka, sojoji sun tabbatar da cewa suna daf da kawo karshen Turji, wanda ya addabi Zamfara, Katsina da yankunan kewaye da hare-hare, garkuwa da mutane da satar dabbobi.
