Kwamitin majalisar wakilai mai bibiyar kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya gabatar da bukatar ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya.
Idan wannan kudiri ya tabbata, adadin jihohin Najeriya zai karu daga 36 zuwa 67. An karanta bukatar hakan a zauren majalisar yayin zaman da mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Kalu, ya jagoranta a yau Alhamis.
A cewar kwamitin, jihohin za su kasu kamar haka: Arewa ta Tsakiya (6), Arewa Maso Gabas (4), Arewa Maso Yamma (5), Kudu Maso Gabas (5), Kudu Maso Kudu (4), da Kudu Maso Yamma (7).
