Fitaccen ɗan TikTok na Najeriya, Peller, ya bayyana cewa shi da matarsa za su yi gudun amarci a ƙasashe takwas bayan aurensu.
A cewarsa, wasu daga cikin ƙasashen da suke shirin ziyarta sun haɗa da Dubai, Birtaniya (UK) da Canada, yayin da ya ce burinsa mafi girma shi ne ya kai ziyara New York a Amurka.
A ranar 29 ga Yuli, 2026, Peller da amaryarsa Jarvis sun halasta aurensu ta hanyar ɗaurin aure a kotu, inda abokai da wasu fitattun mutane suka halarta.
A yayin ɗaurin auren, Peller ya ja hankali bayan ya yi martani ga magatakardar aure lokacin da ta yi musu bayani cewa yin wani aure yayin da mutum ke da aure (bigamy) laifi ne da doka ta tanada, wanda hukuncinsa zai iya kaiwa ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da tara ba.
Tun a watan Yuni ne Peller ya nemi auren Jarvis a wani wuri da aka tanada a bakin teku a La Palm Royal Beach Hotel da ke Ghana, inda ta amince da tayin cikin farin ciki.
Bayan mako guda, Peller ya biya sadakin Jarvis a garin Benin, inda ya bayyana cewa wannan shi ne farkon kyakkyawar tafiyarsu ta rayuwa tare, tare da gode wa iyalansu bisa albarka da goyon bayan da suka ba su.
Ma’auratan sun kuma sanar da cewa za a gudanar da bikin aurensu a ranar 1 ga Agusta, 2026.
