Wata mai ƙirƙirar abubuwan sada zumunta, Becca Oluwabukola, ta bayyana yadda amfani da TikTok ya janyo mata rasa aikinta a wani banki bayan an umarce ta da ta yi murabus saboda bidiyon da take wallafawa.
A cikin wani bidiyo da ta wallafa a TikTok, Becca ta ce bankin ya zarge ta da nuna wani sashe mai muhimmanci na ofishin bankin a cikin wani bidiyon da ta ɗauka yayin aikinta.
Sai dai ba ta bayyana sunan bankin da take aiki ko matsayinta a cikinsa ba. An fi saninta da wallafa bidiyoyin da ke nuna yadda take gudanar da aikinta na yau da kullum.
Becca ta ce ta fara ƙirƙirar abubuwan TikTok tun shekarar 2018, kuma saboda ba ta da wuri mai kyau a gida, tana zuwa ofis da sassafe domin ɗaukar bidiyo kafin fara aiki.
Ta bayyana cewa a shekarar 2022 ta yi amfani da wani sauti da ke magana kan ƙarancin ƙarin albashi, lamarin da ya sa aka kira ta daga hedikwatar bankin tare da yi mata tambaya kan abin da ta wallafa.
A cewarta, an yi mata gargaɗi cewa abin da ta yi ya saɓa da dokokin amfani da kafafen sada zumunta na bankin. Daga baya an dawo da ita bakin aiki, har ma aka tabbatar da aikinta na dindindin.
Sai dai a shekarar 2026, ta ce ta ci gaba da samun gargaɗi saboda bidiyoyin TikTok da take wallafawa. Bayan ta wallafa wani bidiyon da ya nuna wani ɓangare na ofishin bankin, an sake kiranta tare da zarginta da fallasa wuraren da ba a yarda a nuna ba.
Ta ce duk da cewa ta goge bidiyon kuma ta ba da haƙuri a gaban kwamitin ladabtarwa, daga bisani shugabanta ya sanar da ita cewa an umarce ta da ta yi murabus nan take.
Becca ta ce ta bi umarnin, duk da cewa hakan ya sa ta yi matuƙar baƙin ciki.
Rahotanni sun nuna cewa dokokin Babban Bankin Najeriya (CBN) sun haramta wa ma’aikatan bankuna nuna wuraren tsaro, bayanan sirri na kwastomomi, tsarin cikin gida da sauran bayanan da ka iya jefa banki ko kwastomomi cikin haɗari ba tare da izini ba. Wannan na daga cikin matakan kare tsaro da sirrin ayyukan bankuna.
