Dakarun Operation HADIN KAI (OPHK) tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Mafarautan Jihar Yobe sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu a ayyukan garkuwa da mutane a ƙauyen Jegalari da ke Ƙaramar Hukumar Fune ta Jihar Yobe.
A cewar sanarwar rundunar, an gudanar da samamen ne a ranar 23 ga Yuli, 2026, bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargin.
Rundunar ta ce dakarun Bataliya ta 233 da ke sansanin soja na Damaturu ne suka jagoranci farmakin, wanda ya kai ga cafke mutanen biyar tare da ƙwato makamai da wasu kayayyaki da ake zargin suna amfani da su wajen aikata laifuka.
Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku da aka ƙera a gida, bindiga ƙirar pistol guda ɗaya da aka ƙera a gida, alburusai iri-iri da kuma wayoyin hannu guda huɗu.
Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da tsare waɗanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwato domin gudanar da bincike, da nufin tabbatar da rawar da suka taka a laifukan garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta’addanci.
Operation HADIN KAI ta sake jaddada aniyarta na ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri domin hana ‘yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka samun damar gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas.
Hakazalika, rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da kai rahoton duk wani mutum ko motsi da ake zargi ga hukumomin tsaro, tana mai cewa sahihan bayanai daga jama’a na taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.
