Ma’aikatar Man Fetur ta ƙasar Iran ta bayyana cewa ta samu nasarar sayar da man fetur da ya kai darajar dala biliyan 18 a lokacin yaƙi da kuma lokacin tsagaita wuta da Amurka.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na hukuma, ta ce ta samu dala biliyan 11.5 daga sayar da man fetur yayin yaƙin, sannan ta ƙara samun dala biliyan 6.5 a lokacin tsagaita wutar da daga bisani ta rushe a farkon wannan watan.
Ma’aikatar ta ce kuɗaɗen da aka samu sun kai fiye da kashi 60 cikin 100 na kuɗaɗen shiga da aka yi hasashe za a samu daga man fetur a kasafin kuɗin shekarar, duk da halin da ƙasar ta tsinci kanta na rikici.
Sai dai a ƙarshen watan Yuni, Kakakin Majalisar Dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa Iran ba ta iya fitar da man fetur ko kaɗan saboda matakan da Amurka ta ɗauka na hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tashoshin jiragen ruwan ƙasar.
Yaƙin ya ɓarke ne bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran a ranar 28 ga Fabrairu, lamarin da ya sa Iran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan abokan hulɗar Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.
An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Afrilu, wadda ta rage zafin rikicin na wani lokaci. Sai dai rikicin ya sake ɓarke a farkon watan Yuli yayin da ɓangarorin biyu ke ci gaba da takaddama kan ikon sarrafa mashigin ruwan Strait of Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar man fetur a duniya.
