Kungiyar Northern Christian Association (NCA) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan yadda aka ware Naira biliyan 8.05 domin ayyukan coci da masallatai a cikin Kasafin Kudin 2026, tana mai cewa akwai babban bambanci a rabon kudaden.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Rev. Joseph John Hayab, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, kungiyar ta bayyana cewa ba ta adawa da tallafin gwamnati ga ayyukan addini, amma dole ne a gudanar da hakan bisa ka’idojin adalci, gaskiya da daidaito kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Kungiyar ta ce rahotanni sun nuna cewa an ware kimanin Naira biliyan 1.91 domin ayyuka guda bakwai da suka shafi coci-coci, yayin da aka ware Naira biliyan 6.14 domin ayyuka guda 52 da suka shafi masallatai.
NCA ta bayyana cewa wannan babban bambanci ya kara haifar da damuwa a tsakanin Kiristoci, inda ta ce hakan na nuna alamun rashin daidaito da nuna bangaranci wajen aiwatar da manufofin gwamnati.
Kungiyar ta kara da cewa Kiristocin Najeriya sun dade suna nuna hakuri da juriya domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasa, amma gwamnati na ci gaba da daukar wannan hakuri a matsayin rauni.
Ta ce nuna son kai, rashin adalci da rashin daidaito wajen mu’amala da ‘yan kasa na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rarrabuwar kawuna, rashin amana da kuma raunana hadin kan Najeriya.
Saboda haka, kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta fito fili ta bayyana dalilin wannan bambanci wajen rabon kudaden, tana mai jaddada cewa kundin tsarin mulkin kasa ya ba kowane dan Najeriya hakkin samun kulawa iri daya ba tare da la’akari da addininsa ba.
NCA ta kuma bayyana cewa matsayinta ba yana nufin adawa da Musulunci ko Kiristanci ba ne, ko kuma adawa da hadin gwiwar gwamnati da kungiyoyin addini, sai dai kira ne ga tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya wajen aiwatar da manufofin gwamnati.
A karshe, kungiyar ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta sake duba rabon kudaden domin tabbatar da adalci da daidaito, tana mai cewa duk wani tsari na gwamnati da kasafin kudi ya kamata ya karfafa hadin kan kasa tare da kara wa ‘yan kasa kwarin gwiwa kan cewa gwamnati na gudanar da mulki ba tare da nuna bangaranci ba.
