Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana damuwarsa kan yadda hukumar ke rasa ƙwararrun ma’aikatanta sakamakon ƙarancin albashi da walwala, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027.
Da yake jawabi a Abuja yayin ziyarar girmamawa ga Shugaban Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga da Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi (RMAFC), Dakta Mohammed Bello Shehu, Amupitan ya roƙi gwamnati da ta ƙara wa INEC kuɗaɗen gudanarwa tare da inganta jin daɗin ma’aikata.
Ya bayyana cewa a cikin ‘yan shekarun nan, hukumar ta rasa wasu ƙwararrun ma’aikata saboda komawa wasu wuraren aiki da ke ba da albashi mai kyau, yayin da da dama daga cikin manyan jami’ai kuma ke dab da ritaya.
A cewarsa, inganta albashi da walwala zai taimaka wajen riƙe ƙwararrun ma’aikata, ƙara musu ƙwarin gwiwa, da kuma ƙarfafa amincewar al’umma da tsarin zaɓe.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa ayyukan hukumar ba su tsaya ga gudanar da zaɓe kaɗai ba, har da rajistar masu kaɗa ƙuri’a, rajistar jam’iyyun siyasa, da kula da duk wasu harkokin da suka shafi zaɓe kafin da bayan gudanar da shi.
Ya ƙara da cewa zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Tarayya za a gudanar da su ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi za su gudana ranar 6 ga Fabrairu, 2027. Haka kuma, ya sanar da cewa zaɓen gwamnan Jihar Osun zai gudana ranar 15 ga Agusta, 2026.
A nasa martanin, Shugaban RMAFC, Dakta Mohammed Bello Shehu, ya yaba da irin gudummawar da INEC ke bayarwa wajen gudanar da zaɓe tun daga shekarar 1999, tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da samun goyon baya domin tabbatar da nasarar zaɓen 2027.