Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar daukar wasu matakai kan kamfanonin Afirka ta Kudu da ke gudanar da kasuwanci a Najeriya idan hare-haren kyamar baki da ake yi wa ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu suka ci gaba.
Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta bayyana hakan yayin da take magana kan yadda ake ci gaba da muzgunawa da kuma kai hare-hare kan ‘yan Najeriya da ke zaune a kasar Afirka ta Kudu.
Ta ce duk da cewa Najeriya ta dade tana bin hanyoyin diflomasiyya da tattaunawa wajen warware matsalar, gwamnati na iya sake nazarin wasu zabuka idan har ba a kawo karshen hare-haren ba.
A cewarta, akwai sama da kamfanonin Afirka ta Kudu 120 da ke gudanar da harkokinsu a Najeriya, kuma babu wanda ke muzgunawa ma’aikatansu ko hana su gudanar da kasuwanci.
“Ba wanda ke tambayar ma’aikatan kamfanonin Afirka ta Kudu a Najeriya ko su ‘yan Afirka ta Kudu ne ko ‘yan Najeriya. Ba wanda ke kwace musu shaguna ko kasuwancinsu. Amma wannan shi ne abin da ke faruwa ga ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu,” in ji ta.
Ta ambaci manyan kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Najeriya kamar MTN, MultiChoice, Stanbic da Protea, tana mai cewa gwamnati za ta iya duba hanyoyin da suka dace domin kare muradun ‘yan kasarta.
Sai dai ministar ta jaddada cewa duk wani mataki da za a dauka dole ne ya bi kundin tsarin mulkin kasa da kuma hanyoyin doka da majalisa ta tanada.
Ta bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin Najeriya na ci gaba da tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu ta hanyar diflomasiyya, yayin da Majalisar Dokoki za ta taka muhimmiyar rawa idan har aka bukaci daukar wasu matakai na gaba.
Bianca Odumegwu-Ojukwu ta kuma bayyana cewa hukumomin Afirka ta Kudu sun yi watsi da yarjejeniyar fahimtar juna da suka kulla da Najeriya a watan Oktoban 2025 domin samar da tsarin gargadin gaggawa da kariya ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasashen biyu yayin rikice-rikice.
Ta ce abin damuwa ne yadda wasu ‘yan Najeriya da suka shafe shekaru suna rayuwa a Afirka ta Kudu, ciki har da wadanda suka auri ‘yan kasar kuma suka haifi yara a can, ke fuskantar matsin lambar barin kasar tare da iyalansu.
Tun a watan Mayun bana, Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bukaci a soke lasisin wasu kamfanonin Afirka ta Kudu da ke aiki a Najeriya, ciki har da MTN da MultiChoice, sakamakon sabbin hare-haren kyamar baki da ake yi wa ‘yan Najeriya a kasar.
Lamarin na ci gaba da janyo muhawara, yayin da ake kira ga gwamnatocin kasashen biyu da su nemo mafita cikin gaggawa domin kare rayuka, dukiyoyi da kuma kyakkyawar alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu
